Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
Published: 14th, May 2025 GMT
Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar.
Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai.
Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a kai, tare da mayar da hankali wajen habaka bukatu na cikin gida ta yadda ta kaucewa dogaro da kasashen waje, yayin neman ci gaba. Don haka duk wani matsi na Amurka, sai ya fi tasiri kanta maimakon kasar Sin. A ganina, wannan dalili ne ya sa Amurka neman sulhu ta hanyar neman tattaunawa da kasar Sin. Za mu iya cewa, ana maraba da tattaunawar duk da dama can Sin ta sha cewa, yaki ba zai samar da mafita ba, kuma kofarta a bude take a tattauna bisa adalci da sanin ya kamata.
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A KanoBisa la’akari da karfinsu na tattalin arziki, Sin da Amurka na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin duniya da ma harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma tattaunawa ta baya bayan nan da kasashen biyu suka yi za ta taka rawa gaya wajen rage sabanin dake tsakaninsu da aza tubalin zurfafa hadin gwiwa.
Hakika yadda Sin ta tsaya kai da fata, ita ce kadai hanya ta nuna wa Amurka cewa fin karfi ba zai haifar da da mai ido ba, kuma tabbas hakan ya kwatar wa kasashen duniya musamman masu tasowa ’yanci, tare da ba su kwarin gwiwar bijirewa cin zali. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran : harin da Isra’ila ta kai ‘ ayyana yaki’ ne_ Araghchi
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka a kan kasar tamkar shelanta yaki ne.
Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban sakatare na MDD da kuma shugaban kwamitin sulhu bayan da Isra’ila ta kai munanan hare-hare kan wuraren soji da cibiyoyin nukiliya da kuma wuraren zama wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), masana kimiyyar nukiliya da fararen hula na iran.
“Wadannan ayyuka na zalunci ba wai kawai sun zama babban cin zarafi ne ga ‘yancin kan kasar Iran a matsayinta na mamba mai cin gashin kanta a Majalisar Dinkin Duniya ba, amma kamar yadda dokokin kasa da kasa da dokokin jin kai na duniya, ciki har da yarjejeniyar Geneva, suka tanada wannan na daga cikin ayyukan wuce gona da iri da laifukan yaki.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sauke nauyin da ke wuyansa, ya yi kakkausar suka ga wannan ta’addanci tare da daukar matakin gaggawa kan Isra’ila.
Ya kara da cewa “Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi aiki da cikakkiyar azama wajen kare ‘yancinta, al’ummarta da kuma tsaron kasarta. Wannan wani hakki ne da ba za a iya tattaunawa da shi ba.”
Daga cikin hare-haren da ta kai, Isra’ila ta kai hari kan Cibiyar Nukiliya ta Natanz da ke tsakiyar kasar Iran, wadda ke aiki karkashin cikakken kulawar Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), in ji shi.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi gargadin cewa hare-haren ta’addanci na gwamnatin Tel Aviv na jefa rayuwar fararen hular Iran cikin hadari tare da haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.