Aminiya:
2025-05-13@10:48:28 GMT

Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno

Published: 13th, May 2025 GMT

Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno.

Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin.

Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “ISWAP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda runduna ta 24 take.

Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A

“’Yan ta’addan sun ƙona tankokin yaƙi kuma sun kwashi makamai daga sansanin sojin,” in ji shi.

Wani mazaunin Marte, gari mai nisan kilomita 38 daga Dikwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Dikwa, ya ce sun ji karar harbe-harben kuma daga bisani suka ga jirgin soji yana shawagi.

Ya ce, “mun samu labarin cewa an tura ƙarin jami’an tsaro kuma an ƙwato sansanin sojin, amma ’yan ta’addan sun sun sace makamai kuma sun koma motoci da rumbun makaman sojin da ke wurin.”

Ya ci gaba da cewa, “abin takaici mayaƙan sun tsare mata da ƙananan yara da dama a Sabon Marte, amma wasu da dama sun samu tserewa zuwa Dikwa domin tseratar da rayuwarsu.

“Ba a daɗe ba da ’yan ƙungiyar suka kai hari a Malam Fatori, inda suka kashe sojoji 21 da wani daga cikin kwamdojinmu.”

Daga watan Janairu zuwa yanzu an kai wa sansanonin soji da dama hare-hare a yankin Tafkin Chadi da kuma Dutsen Mandara da ke Dajin Sambisa a jihohin Borno da Yobe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Marte tankokin yaƙi

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO

Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa.

Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance.

Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin.

Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO?

NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannann rana zai yi duba.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Wani Sansanin Yan Gudun Hijira A Gaza
  • Kwalara ta yi ajalin mutum 4 a Filato
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kwato Makamai A Borno
  • HKI Ta Kai Hare Hare Kan Wani  Sansanin Yan Gudun Hijira A Yamma Da Kogin Jordan
  • NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO
  • Yadda ɓallewar ƙasashen AES ta illata ECOWAS
  • Iran Ta Musanta Zargin Kamfanin Dillancin Labaran Reuters Dangane Da Aikawa Rasha Makamai
  • Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu
  • Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso