Sojojin HKI Sun Sake Yin Kisan Kiyashi Mai Firgitarwa A Cikin Asibitin Gaza
Published: 14th, May 2025 GMT
A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama.
Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin Khan-Yunus.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci.
Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a cikin sansanoni dake cike da Falasdinawan da aka raba su da gidajensu saboda yaki da suke daura da asibitin.
Gwamman Falasdinawa ne dai su ka yi shahada,kuma wasu gwamman majiyyatan suna a karkashin baraguzan gininin asibitin da ya fada a kansu.
Masu ayyukan ceto sun sanar da tsamo shahidai 28 da kuma wadanda su ka jikkata su 70,kamar yadda mai Magana da yawun kungiyar Muhammad Basal ya ambata.
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda 6, da hakan ya haddasa rusau mai yawa akan ginin asibitin.
Tuni dai masu tafiyar da asibitin su ka sanar da cewa, ba za su iya karbar wadanda su ka jikkata ba.
An dauki marasa lafiya da kuma wadanda su ka jikkata zuwa asibitin “Nasir” wanda shi ma bangarensa mafi girma ya rushe.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp