Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon nazari da aka yi kan mutane 2,500 a fadin kasashe 10 na Latin Amurka.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, masu bayar da amsa sun amince da manufa da nasarorin da aka cimma na zamanantar da kasar Sin, tare da gamsuwa da dangantakar Sin da kasashen Latin Amurka. Al’ummar Sin da Latin Amurka mai makoma ta bai daya na kara samun goyon baya daga mutanen yankin Latin Amurka.

Kasashen Sin da na Latin Amurka dukkansu masu tasowa ne kuma muhimman abokan hulda dake hadin gwiwa bisa daidaito da moriyar juna da neman ci gaba na bai daya. Manufar zamanantar da kasar Sin ta ba kasashe a Latin Amurka wani misali mai daraja yayin da suke kokarin neman ci gaba. Nazarin ya nuna cewa, galibin wadanda suka bayar da amsa na da kyakkyawan ra’ayi game da kasar Sin, inda kaso 94.8 ke ganinta a matsayin wadda ta samu nasara. Kaso 85.9 kuma suna sha’awarta, sannan kaso 94.8 na kallonta a matsayin wadda ke da karfin tattalin arziki, sai kaso 91 da suka yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka cikin lokaci mai tsawo.

A matsayinta na mai ingiza hadin gwiwar Sin da Latin Amurka, tasirin shawarar Ziri Daya da Hanya daya a kasashen Latin Amurka yana karuwa, kuma yadda masu bayar da amsa suke fahimtar shawarar, shi ma yana karuwa. A bayanin shawarar, masu bayar da amsa sun bayyana ra’ayinsu game da muhimman batutuwa 3 dake cikin yarjejeniyar shawarar, inda matsayin shawarar na samar da wani tsari da kasashe za su runguma domin inganta tattalin arziki ya samu goyon baya da kaso 55. Matsayinta na wani muhimmin abu da Sin ta gabatar domin kyautata tsarin jagorantar harkokin duniya ya samu kaso 54, yayin da burin Sin na hada gwiwa da sauran kasashe ya samu kaso 52.6. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: bayar da amsa

এছাড়াও পড়ুন:

Putin ya ba da shawarar tattaunawa kai tsaye da Ukraine a Istanbul

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul.

A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin.

Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata kafa sulhu ya zama wani bangare na tattaunawa kai tsaye kan rikicin da aka shafe sama da shekaru uku ana yi.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da shawarar Vladimir Putin na tattaunawa tsakanin Moscow da Kyiv a Istanbul, in ji fadar shugaban kasar Turkiyya.

“A yayin tattaunawar, shugaba Erdogan ya shaidawa shugaba Putin na Rasha cewa, a shirye Turkiyya ta ke ta karbi bakuncin tattaunawar da za ta kai ga cimma matsaya mai dorewa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Kasuwanci: Sanarwar Da Sin Da Amurka Suka Fitar Muhimmin Mataki Ne Na Warware Sabaninsu
  • Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
  • Iran Da Amurka Sun Fahinci Juna Sosai A Zagaye Na 4 A Tattaunawa A Mascat
  • Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
  • Putin ya ba da shawarar tattaunawa kai tsaye da Ukraine a Istanbul
  • Tehran ta bayyana aniyarta na karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda da Nijar
  • Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
  • Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu
  • Yemen Tana Bukukuwan Samun Nasara Kan Amurka Kuma Zata Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Gaza