Za A Samar Da Na’urar Kula Da Lafiyar Zuciya A Jami’ar Dan Fodio Da Ke Sakkwato
Published: 13th, May 2025 GMT
Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewar ministan, wadannan kayan aiki na zamani za su taimaka matuka wajen aikin gano cutar da kuma warkar da cututtukamasu alaƙa da zuciya.
Ya bayyana cewa hakan wani mataki ne na gwamnatin tarayya don ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na musamman a yankin Arewa maso Yamma da kuma rage bukatar zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya.
“Asibitin koyarwa na jami’ar Sakkwato yanzu zai samu damar ba da kulawa ta gaggawa da ke ceton rai ga masu fama da cututtukan zuciya”.
Hakan na da matukar muhimmanci ga jihar Sokoto da daukacin yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya, wanda zai dakile zirga-zirgar fita ƙasashen waje domin jinya ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiyarmu na gaba,” in ji Pate.
Ya ƙara da cewa wannan matakin yana cikin jerin shirye-shiryen da ake aiwatarwa don samar da kayan aiki na zamani a asibitocin koyarwa na tarayya domin bincike, magani da horarwa, bisa tsarin sauye-sauyen da ake yi a fannin lafiya karkashin jagorancin Shugaba Bola TinuTinubu.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lafiyar Zuciya Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
Ministan wajen na Sin, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa, ciki har da Switzerland, ta yadda za a kai ga cimma nasarar aiwatar da sahihan matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA