Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe
Published: 13th, May 2025 GMT
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.
Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran zai kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya a yankin.
An yi hakan ne da nufin bai wa jama’a damar samun kula da lafiya mai inganci cikin sauki, domin inganta jin dadinsu baki daya.
A shirye-shiryen kaddamar da shirin, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Majalisar, Honarabul Bashir Adamu Nababa, ya gana da Darakta-Janar na KADCHMA, Mallam Abubakar Hassan, inda suka tattauna kan muhimman matakai na aiwatarwa, sannan aka mika fom din rajista domin raba su ga wadanda aka zaɓa a cikin gundumar Makera.
A bayaninsu, jami’an shirin sun jaddada kudurin shugaban majalisar na ganin al’umma ta amfana, inda suka bayyana wannan tsarin kiwon lafiya a matsayin wata shaida ta jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima.
Ana sa ran cewa shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na gundumar za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da rajistar cikin sauki da gaskiya a cikin makonni masu zuwa.
Shamsuddeen Munir Atiku