Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata.

Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya.

Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban HKS kuma shugaban gwamnatin riko na kasar ta Siriya bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-Asad ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatinsa zata samar da huldar Jakadanci da HKI.

Abu Muhammad Al-jula ne, ya kuma gabatar da wani shiri na gina Hasumiyyar Trump a birnin Damascus babban birnin Kasar Siriya don yabawa shugaban.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Siriya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.

 

A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda 10 kamar yadda ta bayyana: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.

 

Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka
  • Giyar mulki Na Jan Trump – Ƴan Democrats
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 
  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
  • HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya
  • An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata
  • Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho
  • Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa