‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hari Kan Gidan Yarin Al-Obeid Tare Da Kashe Fararen Hula Masu Yawa
Published: 12th, May 2025 GMT
Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan
Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid.
Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki.
Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru a gidan yarin Al Obeid, babban laifin yaki ne, wanda ya kara tabbatar da cewa: Dakarun Kkai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da magoya bayansu ‘yan ta’adda ne da suke cin zarafin fararen hula a Sudan.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?
A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai a cikin babbar shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a watan jiya.
Yayin da ake kawo karshen tsohon zamanin da kasashen yammacin duniya ke taka rawa a matsayin masu ba da umarni a duniya, kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka da kasar Sin, za su kara kawo ci gaba mai inganci, da adalci, da daidaito ga duniya, yayin da suke kokarin aiwatar da wasu sabbin tunani, gami da raya su a kai a kai. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA