Shugaban Kungiyar Hizbulla Ya Ce Cewa Kungiyarsa Ba Zata Taba Mika Kai Ga Bukatun HKI Ba
Published: 13th, May 2025 GMT
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa gwamnatin kasar Lebanon don kawo karshen kungiyar ba.
Tashar talabijin ta Almanar ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya litinin, a wanijawabinda ya yi ta tashar talabijin ta AL-Amnar na kungiyar don tunawa da babban kwamandar kungiyar Sayyed Mustafa Badreddin wanda yayi shahada shekaru 9 da suka gabata.
Sheikh Kasim ya kara da cewa kungiyar tana kan al-kawalinda na tsagaita budewa juna wuta duk tare da cewa HKI ta keta wannan yarjeniyar har sau 3000.
HKI dai ta amince da tsagaita budewa juna wuta bayan fafatawa da kungiyar Hizbullah na tsawon watanni 14, a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kudancin kasar Lebanon.
Sannan bayan ta rasa daruruwan sojojinta a kan iyakar kasar Lebanon wadanda suka dauki kimani watannin 2 suna kokarin shiga kasar ta Lebanon daga kudancin kasar tare da tankunan yakin Mirkava, amma suka kasa yin hakan.
Sheikh Kasin ya bayyana cewa dukkan kokarin HKI da Amurka na shafe al-ummar Falasdinawa a Gaza ko a yankin yamma da kogin Jordan ba zai kai ga nasara ba. Duk da cewa manufarsu ta shafe kasar Falasdinu daga doron kasa ne fiye da shekaru 75 da suka gabata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya.
Trump zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine tare da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyid Urdugan.
Shugaban yana zuwa yankin ne a dai-dali lokacinda HKI ta ci gaba da kissan kiayashi ga Falasdinawa a Gaza da kuma hana abinci shiga Gaza.
Shugaban ya sami labarin saken wani ba’amerike mai suna Edan Alezander wanda yake tsare a hannun kungiyar Hamas tun shekara ta 2023. Kungiyar Hamas ta sake shi ne don ganin HKI ta bude kofar Rafah don a shigo da kayakin abinci ga falasdinawa wadanda suke fama da yunwa. Tun kimani watanni biyu da suka gabata.
Shugaban yace yana saran kulla yarjeniyoyi na zuba jari a Amurka da kuma harkokin kasuwanci a wannan tafiyar.