Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha
Published: 13th, May 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.
Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran zai kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya a yankin.
An yi hakan ne da nufin bai wa jama’a damar samun kula da lafiya mai inganci cikin sauki, domin inganta jin dadinsu baki daya.
A shirye-shiryen kaddamar da shirin, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Majalisar, Honarabul Bashir Adamu Nababa, ya gana da Darakta-Janar na KADCHMA, Mallam Abubakar Hassan, inda suka tattauna kan muhimman matakai na aiwatarwa, sannan aka mika fom din rajista domin raba su ga wadanda aka zaɓa a cikin gundumar Makera.
A bayaninsu, jami’an shirin sun jaddada kudurin shugaban majalisar na ganin al’umma ta amfana, inda suka bayyana wannan tsarin kiwon lafiya a matsayin wata shaida ta jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima.
Ana sa ran cewa shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na gundumar za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da rajistar cikin sauki da gaskiya a cikin makonni masu zuwa.
Shamsuddeen Munir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kiwon Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
Ministan wajen na Sin, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa, ciki har da Switzerland, ta yadda za a kai ga cimma nasarar aiwatar da sahihan matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA