Iran ta yi tir da sabbin takunkumin ‘rashin adalci’ da Amurka ta kakaba mata
Published: 13th, May 2025 GMT
Iran ta yi tir da sabbin takunkuman da ta danganta da na rashin adalci da Amurka ta kakaba mata.
Amurka dai ta kakaba wa Iran sabbin takunkuman, ne duk da ci gaba da tattaunawar nukiliyar da ake yi tsakanin kasashen biyu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana wasu ‘yan kasar Iran guda uku da wani kamfani mai suna Fuya Pars Prospective Technologists, bisa zargin cewa suna da hannu wajen gudanar da bincike da kuma ayyukan da suka shafi makaman nukiliya.
Amurka, ta ce takunkumin ya shafi toshe duk wasu kadarori na mutanen a Amurka tare da hana mu’amalar kasuwanci da su.
Sabon takunkumin ya zo ne kwana guda bayan Iran da Amurka sun gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da nufin kulla sabuwar yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran da kuma cire takunkumin da aka kakabawa Tehran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Amurka Sun Fahinci Juna Sosai A Zagaye Na 4 A Tattaunawa A Mascat
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya gabatar bayan kammala zagaye na 4 na tattaunawar a jiya.
Ministan y ace bangarorin biyu sun tattauna babututuwan da suke da zurfi a cikin matsalolin da kasashen biyu suke son su warware, na farko gamsar da Amurka kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran ban a tsaro bane. Da kuma maganar daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.
Yace tattaunawar jiya yafi magana a kan bayanai masu zurfi kan wadanan matsaloli biyu da sannan babu batun magana ta sama sama.
Steve Witkoff mai bawa shugaban kasar Amurka shawara a kan al-amuran gabas ta tsakiya ne ya jagoranci tawagar Amurka kuma ministan harkokin wajen Omman ne mai kai kawo tsakanin bangarorin b iyu.
Tun ranar 12 ga watan Afrilu ne aka fara tattaunawa ba kai atsaye ba tsakanin Amurka da iran kan shirinta na makamashin nukliya ba kai tsaye ba. Bayan da Amurka ta rubutawa Iran wasika dangane da hakan.