Majalisar Nasarawa Ta Bukaci Gwamnati Ta Kai Dauki Ga Wadanda Iftila’in Guguwa Ya Shafa
Published: 14th, May 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar.
Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki.
Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane da dama.
“Ina godiya da wannan kuduri da Hon. Hudu A Hudu ya gabatar domin wannan iftila’in ya shafi mazabata kai tsaye, inda guguwar ruwan ta rushe dakin jarrabawa na GSS Bassa. Har ila yau, kusan dukkan mazabu a fadin jihar sun fuskanci wannan matsala kamar yadda yawancin ‘yan majalisa suka bayyana.
“Shawarar mu ita ce, dukkan shugabannin kananan hukumomi 13 na jihar su tattara bayanan gine-gine da mutanen da abin ya shafa tare da nemo hanyoyin da za a tallafa musu.
“Muna kira ga Mai Girma Gwamna da ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar NASEMA da ta gaggauta daukar mataki ta hanyar raba kayayyakin tallafi ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.
Har ila yau, majalisar ta bayyana cewa guguwar ta bar iyalai da dama cikin kunci yayin da wasu ke kwance a asibitoci.
Tunda farko, Honarabul Hudu A Hudu, dan majalisa mai wakiltar Mazabar Awe Arewa, yayin da yake gabatar da batun, ya ce al’ummar Mahanga da ke mazabarsa da wasu yankuna sun rasa matsugunansu sakamakon guguwar.
“Wannan lamari ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum matuka, inda gidaje fiye da 30 da mutane 500 suka samu matsala.
“Ina kira gare ku da ku goyi bayan wannan kuduri domin gwamnati ta zo ta taimaka wa mutanena.” Inji shi
Daga Aliyu Muraki
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga
Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.
Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.
Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp