HausaTv:
2025-10-13@18:01:42 GMT

 Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Talata

Published: 13th, May 2025 GMT

A daidai lokacin da  sake bude yaki a Gaza ya cika kwanaki 57,sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare akan al’ummar Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama.

Cibiyar watsa labaru ta Falasdinu ta sanar da cewa; Sojojin na HKI sun kai hare-hare masu yawa a sassa mabanbanta na gaza wanda ya fara tun daga watan Maris, da hakan ya kara jefa Falasdinawa cikin wahala, bayan yunwar da suke fama da ita.

Da safiyar yau Talata sojojin na HKI sun kai hare-hare  sau 3 a garin Abasan a gabashin Khan-Yunus.

A cikin birnin Gaza kuwa sojojin na HKI sun baje wasu gidaje da kasa a karo na uku.

A garin Khan-Yunsu wani matashi mai suna Amid Hamdun al-Qudrah, ya yi shahada.

A unguwar “Shuja’iyyah” ma wani Bafalasdine mai suna Muhammad Mu’in  al-Ja’abari ya yi shahada sanadiyyar raunin da ya samu a harin baya.

A unguwar “Zaytun” kuwa sojojin na HKI su kai hare-hare ne har sau 8 a yau Talata.

A daren jiya wasu Falasdinawa 3 daga iyali 1 sun yi shahada a cikin tantin ‘yan hijira a yankin ‘al’amudi’ a arewacin Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kai hare hare

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth October 12, 2025 Daga Birnin Sin An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje October 12, 2025 Daga Birnin Sin Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace October 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa
  • Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin