‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi
Published: 14th, May 2025 GMT
Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu.
CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami.
Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo na musamman sun kammala a makon jiya, sannan kuma rundunar ta ƙaddamar da sabbin dabarun yaƙi da laifuka kamar sintiri a manyan hanyoyi, kai samame maɓoyar ‘yan daba, da kuma binciken motocin jama’a a wurare daban-daban.
Ya ƙara da cewa rundunar tana aiki da al’umma ta hanyar amfani da tsare-tsaren ‘yansanda.
Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Jihar Kogi, musamman sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki, da su ba mi wa ‘yansanda goyon baya domin a samu zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya roƙi haɗin kan jama’a don kare rayuka da dukiyoyinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yansanda
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Soke Yin Jawabi Ga ‘Yan Kasa Na Ranar Dimokuradiyya, Zai Yi Daga Zauren Majalisa
Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin yi wa ‘yan kasa jawabi kai tsaye da aka shirya gudanarwar tun farko a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, domin tunawa da cikar ranar dimokradiyyar Nijeriya shekaru 26. A maimakon haka, zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar. An bayyana sauyin ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ofishin SGF, Segun Imohiosen ya fitar a ranar Laraba. Amma Duk da haka, sauran shirye-shiryen ranar Dimokradiyya za su ci gaba da gudana kamar yadda aka sanar a baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp