HausaTv:
2025-05-13@20:42:50 GMT

Amurka ta kulla yarjejeniyar sayen makamai ta dala biliyan 142 da Saudiyya

Published: 13th, May 2025 GMT

Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya.

Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki.

Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi girma a tarihi.

” Wannan yarjejeniya, wacce wani bangare ne na babban kunshin alkawurran saka hannun jari – da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 600, a cewar gwamnatin Amurka – za ta ba wa masarautar Saudiyya damar sayen “kayan aikin soja daga kamfanonin tsaron Amurka goma sha biyu,” musamman a fannin tsaron sararrin samaniya, makamai masu linzami, tsaron teku da tsarin sadarwa.

A wani labarin kuma shugaban kasar ta Amurka ya sanar da dage takunkumi kan kasar Siriya.

“Zan ba da umarnin dage takunkumin da aka kakaba wa Siriya domin ba su dama ta daukaka,” in ji shugaban na Amurka, wanda ke nuni da cewa ya cimma wannan matsaya ne bayan bukatar gaggawar da yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya yi masa.

Ana san kuma zai gana da shugaban rikon kwarya na Siriya Ahmed al-Charaa nan gaba a Saudiyyar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za a taba amincewa da shi ba.

A cikin rashin tabbas da ke tattare da ci gaba da aiwatar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, biyo bayan cin karo da maganganun da jami’an fadar mulkin Amurka ta White House suka yi, da kuma karuwar bukatar Amurka kan Iran; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kawo karshen matsin lambar da ake yi mata; Yayin da shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasarsa da gaske take yi kan tattaunawar, kuma tana neman cimma matsaya, amma neman yin watsi da cibiyoyin nukiliya da fasahar nukiliyar, wani zabi ne da ba zata taba a amincewa da shi ba. Pezeshkian ya jaddada cewa Iran ba ta taba nema ba kuma ba za ta taba neman mallakar makamin nukiliya ba.

Shugaba Pezeshkian ya ce, “Za su iya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman mallakar makaman kare dangi, kuma ba zata taba amincewa da batun yin watsi da dukkan cibiyoyin nukiliya da binciken ilimi da take yi kafin fara tattaunawar ba, kuma tabbas manufarta ta tattaunawan ita ce neman cimma yarjejeniya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria
  • HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya
  • Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
  • Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka
  • Sabuwar Gwamnatin Siriya Zata Kulla Kyakkyawar Alaka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Matakan Cimma Nasarar Sassan Tsaron Kasa
  • Iran Ta Musanta Zargin Kamfanin Dillancin Labaran Reuters Dangane Da Aikawa Rasha Makamai
  • Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta