Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan yara.

M. Baghai ya bayyana cin zarafi da keta hakkin bil’adama da ka’idojin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a yankunan Falasdinawa da gwamnatin sahyoniyawa ta mamaye a matsayin wani babban cin zarafi ga muhimman ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

Ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da shari’o’i a kan gwamnatin Sahayoniya da wakilanta da ke gaban kotun kasa da kasa (ICJ) da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki da kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta harbo jiragen saman yaki kirar F-35

Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi nasarar harbo jiragen yaki kirar F-35, bayan da ta yi nasarar auna wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar F-35 guda biyu, kuma ta barar da su kasa.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da wadannan jirage masu tsananin ci gaban zamani wajen kai hare-haren wuce gona gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Juma’a, wanda hare-haren suka yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an sojan Iran da masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.

Ma’aikatar hulda da jama’a ta rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Dakarun tsaron saman Iran sun harbo jiragen saman yaki kirar F-35 guda biyu, baya ga wasu jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya marasa matuka ciki.

Sanarwar ta nuna cewa: Jami’an tsaron Iran sun kame daya daga cikin matukan jiragen wacce mace ce, kuma ana kan bincike domin sanin makomar matukin daya jirgin.

Abin lura shi ne cewa: Jiragen yakin kirar F-35 da ‘yan sahayoniyya ke amfani da su na daga cikin wadanda suka ci gaba a duniya kuma ake gwada su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
  • Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Kakkabo Jiragen Yakin Isra’ila Biyu Kirar F-35
  • Iran : harin da Isra’ila ta kai ‘ ayyana yaki’ ne_ Araghchi
  • Jagora: Sojojin Iran ba zasu sararawa Isra’ila ba
  • Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran
  • Gwamnan Gombe Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Daba Suka Yi Wa Amadi Kasiran
  • Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar
  • Sakon Jagora : Isra’ila ta jira hukunci mai tsanani bayan hari kan Iran
  • Rundinar IRGC, ta sanar da shahadar babban kwamandanta Manjo Janar Hossein Salami a harin ta’addancin Isra’ila
  • MDD: Adadin ‘Yan Gudun Hijira A Duniya Ya Kai Miliyan 122