Leadership News Hausa:
2025-09-18@03:48:12 GMT

Ko Ina Cikin Gwamnatin Tinubu, Zan Faɗa Wa APC Gaskiya – El-Rufai

Published: 30th, January 2025 GMT

Ko Ina Cikin Gwamnatin Tinubu, Zan Faɗa Wa APC Gaskiya – El-Rufai

Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.”

El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane.

Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.

An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas

Majiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.

“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.

Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).

Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.

Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.

Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi