Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
Published: 13th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya.
Trump zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine tare da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyid Urdugan.
Shugaban yana zuwa yankin ne a dai-dali lokacinda HKI ta ci gaba da kissan kiayashi ga Falasdinawa a Gaza da kuma hana abinci shiga Gaza.
Shugaban ya sami labarin saken wani ba’amerike mai suna Edan Alezander wanda yake tsare a hannun kungiyar Hamas tun shekara ta 2023. Kungiyar Hamas ta sake shi ne don ganin HKI ta bude kofar Rafah don a shigo da kayakin abinci ga falasdinawa wadanda suke fama da yunwa. Tun kimani watanni biyu da suka gabata.
Shugaban yace yana saran kulla yarjeniyoyi na zuba jari a Amurka da kuma harkokin kasuwanci a wannan tafiyar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu
Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco.
Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9.
Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus.
Har’ila yau shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar Brazil Lula de Silva a kan ziyarar da ya kawo kasar Rasha, ya kuma kara da cewa danganta tsakanin kasashen biyu yana kara karfi a hankali a hankalai.