Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Wani Sansanin Yan Gudun Hijira A Gaza
Published: 13th, May 2025 GMT
Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei yana fadar haka a jiya Litinin, a jawabinda ta saba gabatarwa a ko wace litinin.
Esmaeil Baghaei ya kara da cewa nauyin MDD ce ta dakatar da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza, kuma kasa yin haka wani abin kunya ne ga majalisar.
Ya kuma kara da cewa ya zama wajini kutunan kasa da kasa wadanda suka hada da ICJ ta MDD da kuma ICC mai hukunta manya-manyan laifuka su yiwa shuwagabanin HKI sharia kan laifukan yakin da suke aikatawa a gaza fiye da shekara guda.
Tun ranar 7 gawatan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin HKI suka fara kaiwa falasdinawa a Gaza hare-hare, ta sama da kasa, da manufar shafe kungiyar wacce take iko da yankin daga doron kasa da kuma kwace yankin gaza daga hannun Falasdinawa. Kuma ya zuwa yanzun sun kashe falasdinawa fiye da 56,000.
Wasu fiye da dubu 107 suka ji rauni. Banda haka tun kimani watanni biyu da suka gabata suna hana shigar da abinci zuwa cikin yankin wanda ya kai ga miliyoyin Falasdinawa a yankin suna fada cikin yunwa maitsanani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Amince Ta Saki Fursinan Yaki Wanda Yake Da Jinsiyar Amurka Da HKI
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi.
Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga Gaza. Da kuma bude kofar Rafa don shigowar kayakin agaji da abinci cikin yankin.
Khalil Al-Hayya ya kara da cewa hamas ta yadda a hada wata tawaga wacce zata gudanar da harkokin shugabanci a yankin.
A wani labarin kuma an tabbatar da cewa Falasdinawa kimani 109,000 ne suka yi shahada a zirin Gaza, tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
Binciken da aka guddanar ya nuna cewa sojojin yahudawna sun kashe falasdinawa akalla tsaknain 77,00-109.