Gwamnatin Netanyahu Tana Yi Wa Gwamnatin Trump Leken Asiri
Published: 13th, May 2025 GMT
Jaridar “Telegraph” da ake bugawa a Birtaniya ta buga labarin dake cewa; gwamnatin Benjamine Netanyahu ta bai wa kungiyar leken asiri ta waje, umarnin bin diddigin abubuwan da gwamnatin Amurka take yi a cikin sarari da boye.
Rahoton ya kuma kara da cewa; Netanyahu yana kokarin fahimtar abubuwan da gwamnatin Donald Trump take yi ne a boye, kuma menene manufofinta.
Da ma a baya, tashar talabijin din “Fox News” ta nakalto tsohon jami’in hukumar leken asirin HKI yana cewa; Donald Trump ya janye taimakon da yake bai wa Tel Aviv.
Har ila yau, jami’in na HKi ya ce; Tel Aviv tana cikin kidima saboda dalilai da dama da su ka hada da kasa sanin yadda za ta yi da Yemen.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Giyar mulki Na Jan Trump – Ƴan Democrats
‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin.
Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi.
‘Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face ‘tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya.
Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta.
Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a tittuna suna aikata miyagun ayyuka kuma dole ya kawo gyara.