An Bude Taron Karawa Juna Sani Akan Makamashin Nukiliyar Iran Karo Na 31 A birnin Mashhad
Published: 13th, May 2025 GMT
A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya.
Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin wanda ya sami halartar masana wannan fage.
Wasu batutuwa da za a tattauna a wurin taron sun kunshi; Bututun tace sanadarin Uranium, shi kanshi makamashin da kuma hanyoyin tafiyar da da kula cibiyoyin dake aikin tace da sarrafa makamashin na Nukiliya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Neja Ta Jaddada Shirinta Na Yaki Da Matsalar Tsaro
Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar
Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron shirye-shiryen babban taron tsaro da za a gudanar a Minna.
Janar Mohammad Bello Abdullahi ya kara da cewa Gwamnati jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bukaci hadin gwiwa daga kowane bangare domin cimma burin da aka sanya a gaba.
A cewarsa, babban taron zaman lafiya da tsaro na farko da za a gudanar a Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago, na da nufin hada kai da muhimman masu ruwa da tsaki a fannin tsaro na matakin karamar hukuma, jiha da na tarayya, domin samo ingantacciyar mafita ga kalubalen tsaro a jihar.
Janar Bello Abdullahi, wanda ya bayyana kafafen yada labarai a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki a yaki da rashin tsaro, ya jaddada cewa sai an hada kai gaba daya ne za a samu nasara.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Jihar Neja, Kwamared Abu Nmodu, ya jaddada cewa akwai bukatar gwamnati ta tantance tsakanin ‘yan jaridu na gaskiya da kuma na bogi, wanda hakan zai taimaka matuka wajen cimma nasarar da ake bukata a jihar, da kuma amfanin al’umma baki daya.
Sakataren yada labarai na Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim, wanda Hamza Mohammed mai kula da harkokin yada labarai na Gwamna, ya wakilta, ya bukaci hadin gwiwa domin ci gaban jihar.
Taken taron zaman lafiya da tsaro na farko a Jihar Neja wanda za a gudanar gobe Laraba 20 ga watan Mayun 2025, shi ne: “Hadin Gwiwa Wajen Gina Tsaro da Zaman Lafiya Domin Kare Jihar Neja.”
Daga Aliyu Lawal