Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula.
Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa a lokacin da suke faɗa.
A shekarar 2016 ne faɗa ya kaure tsakanin abokan biyu a kan wata hular sanyi a lokacin da suka yi wata tafiyar fatauci a Jihar Bauchi.
A yayin zaman kotun, mai gabatar da ƙara, Wahida Isma’il, ta gabatar da shaidu biyar, shi kuma wanda ake tuhuma ya kare kansa.
Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band ABayan sauraron duka bangarorin, alƙalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Musa Karaye, ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun kawo gamsassun hujjojin da ke tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin.
Daga nan kuma ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kisa ta hanyar rataya
এছাড়াও পড়ুন:
Matan Falasdinawa A Gaza Suna Fama Da Yunwa Mai Tsanani Da Kuma Hare-haren HKI
Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI.
Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu.
A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400. Bugu da kari wasu matan da sun kai 14 sun bace ba a gano su ba, sai kuma wasu matan masu ciki da sun kai 60,000 da suke fuskantar hatsari mai tsanani saboda rashin kula da su, da kuma rusa asibitoti da sojojin HKI su ka yi.
A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata mace mai suna Ummu Muhamad da take rayuwa da ‘ya’yanta 7, bayan da maigidanta ya yi shahada sanadiyyar harin sojojin HKI.
Matar ta bayyana cewa, baya ga mijinta da akwai wani daga cikin ‘ya’yanta da ya yi shahada, kuma su da suke a raye suna da bukatuwa da magungunan da samunsu yake yin wahala saboda halin yaki da ake ciki.
Ta kuma bayyana cewa; Muna fama a yunuwa mai tsanani,babu wanda zai taimake mu, kuma fulawar da ake da ita, ta yin burodi ta kare.