Dole Ne Kansiloli Su Shiga Cikin Dukkan Ayyukan Kananan Hukumomin Su – Gwamna Yusuf
Published: 14th, May 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da su tabbatar da cewa Kansilolinsu sun shiga dukkan ayyukan da aka gudanar a kananan hukumominsu .
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da kansilolin kananan hukumomi 484 daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati, da nufin karfafa alaka tsakanin gwamnatin jihar da majalisun kananan hukumomi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa tana da hankali kuma ba ta da almundahana, kuma ba za a amince da duk wani nau’i na almundahana ba.
Ya kuma bukaci kansilolin da su yi aiki tukuru don ganin sun rike amanar da aka ba su.
Gwamnan ya shawarce su da su yi aiki tare da shugabannin su don inganta ilimi, kiwon lafiya, noma, da kuma ci gaban bil’adama.
Gwamna Yusuf ya umurci kansilolin da su fito da ayyukan da za su amfanar da unguwanninsu, wadanda za a aiwatar da su ne domin amfanin kowa da kowa.
Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu Muhammad Tajuddeen ya yabawa kokarin kansilolin kananan hukumomin wajen gudanar da harkokin kananan hukumominsu.
Ya bukace su da su ci gaba da marawa manufofin gwamnati baya tare da tabbatar da sun sanar da masu zabe wadannan manufofin.
Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Falgore, ya shawarci shugabannin kananan hukumomin da su yi aiki tare da shugabanninsu domin cimma manufofinsu.
Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya duba albashi da alawus-alawus na kansilolin kananan hukumomin domin kara musu kwarin gwiwa.
Shugabar Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen Jihar Kano, Hajiya Saadatu Yusha’u, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na taba rayuwar ‘yan Kano ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Shugaban kungiyar kansilan Arewa maso Yamma, Bashir Shehu Achika, ya yaba da kokarin gwamnati mai ci na samar da ababen more rayuwa ga talakawa.
Ya yi nuni da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna jajircewarsa na tallafawa kananan hukumomi ta hanyar ware kudade don gudanar da ayyuka don jin dadin jama’a.
Achika ya roki gwamnatin jihar da ta shirya wani taron karawa juna sani domin bunkasa kwarjinin kansilolin kananan hukumomi domin gudanar da ayyuka masu inganci.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna Abba Kabir Yusuf
এছাড়াও পড়ুন:
Mali : An rushe dukkan jam’iyyun siyasa a hukumance
A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance.
bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar.
An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi.
Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa.
Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.