Nijeriya Ta Biya Dukkanin Bashin IMF Na COVID-19
Published: 13th, May 2025 GMT
Amma sai yanzu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa a hukumance.
Masana tattalin arziƙin sun bayyana cewa kammala biyan wannan bashi wata alama ce ta daidaituwar tsarin kuɗi na ƙasar da kuma yunƙurin rage dogaro da lamuni daga ƙasashen waje.
Wasu sun ce hakan na iya ƙara jawo amincewar ƙasashen duniya da hukumomin ba da lamuni ga Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da ƙoƙarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙi.
Wani ƙarin bayani daga ma’aikatar kuɗi ya ce an biya bashin ne a matakai daban-daban tun daga shekarar 2021, kuma an kammala biya a farkon shekarar 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwalara ta yi ajalin mutum 4 a Filato
Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.
Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol.
’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a KanoGalibin waɗanda ake zargi sun harbu da cutar an killace su a cibiyoyin lafiya a matakin farko daban-daban da kuma Asibitin Cottage inda suke samun kulawar gaggawa.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bokkos, Mista Amalau Samuel Amalau wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna aiki tare da mahukuntan asibitin domin daƙile ƙalubalen
A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ke fama da rashin lafiyar sun fara samun sauƙi yayin da tuni an sallami wasu daga asibiti.
Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya gargaɗi mazauna da su riƙa taka-tsan-tsan wajen kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta domin kaucewa kamuwa da cutar musamman tsaftace jiki, muhalli da kuma uwa-uba abinci.