Aminiya:
2025-10-13@15:49:39 GMT

‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’

Published: 13th, May 2025 GMT

Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata.

Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai.

HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba

Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka a farkon 2025.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashi na ci gaba da zama ƙalubale amma ana sa ran tattalin arzikin Nijeriyar zai haɓaka a wannan shekarar da kashi 3.6.

Nijeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashi, inda Sieneart ya yi gargaɗin cewa dole ne a ɗauki matakan tsuke bakin aljihu da tasarrufin kuɗaɗe bisa doka da oda.

Sienaert ya ce harajin gwamnati ya ƙaru da kashi 4.5 sama da na shekarar da ta gabata, wanda “muhimmiyar nasara” ce, da janye tallafi ga kuɗaɗen ƙasashen waje, da kyautata tsarin karɓar haraji da yawan saka kuɗaɗe a asusun gwamnati suka kawo.

Kuɗaɗen shiga masu yawa da aka samu sun taimaka wajen cike giɓin Kasafin Kuɗi da aka yi hasashen ya kai kusan kashi uku a 2024, daga kashi 5.4 da aka samu a 2023.

Manyan matakan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke ɗauka, ciki har da kawo ƙarshen tallafin mai, da janye tallafi kan wutar lantarki da karya darajar naira har sau biyu, sun ƙara matsa lamba ga farashin kayayyaki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bankin Duniya Bunƙasa Tattalin Arziƙi Hauhawar Farashi Nijeriya tattalin arzikin

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.

Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.

“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.

RN

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
  • Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
  • Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida