Aminiya:
2025-05-13@19:34:50 GMT

HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya

Published: 13th, May 2025 GMT

Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda tuni ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One.

Shugaban na Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri.

Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano

Trump zai gana ne da Mohammed bin Salman a filin jirgin sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a kusa da hotunan wasu daga ckin mambobin iyalan sarauta na Saudiyya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ma zai kasance a cikin taron.

Bayan Saudiyya, Trump dai na shirin kai ziyara ƙasashen Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa daga ranar Talata zuwa Alhamis na wannan makon.

Shugaban Amurkan na wannan ziyara ta kwanaki huɗu a ƙasashen Gabas ta Tsakiya domin yauƙaƙa dangantaka da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikin makamai na biliyoyi har ma da tattaunawa kan batun yakin Gaza da shirin nukiliyar Iran.

Mista Trump na tare da attajirin Amurka kuma shugaban kamfanin ƙera motocin Tesla, Elon Musk da kuma wasu manyan muƙarraban gwamnati.

Wannan ce ziyararsa ta biyu tun bayan hawu kan karagar mulkin Amurka baya ga halartar jana’izar tsohon shugaban Darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis a birnin Rome na ƙasar Italiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gabas ta Tsakiya Qatar Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Netanyahu Tana Yi Wa Gwamnatin Trump Leken Asiri

Jaridar “Telegraph” da ake bugawa a Birtaniya ta buga labarin dake cewa; gwamnatin Benjamine Netanyahu ta bai wa kungiyar leken asiri ta waje, umarnin bin diddigin abubuwan da gwamnatin Amurka take yi a cikin sarari da boye.

Rahoton ya kuma kara da cewa; Netanyahu yana kokarin fahimtar abubuwan da gwamnatin Donald Trump take yi ne a boye, kuma menene manufofinta.

Da ma a baya, tashar talabijin din “Fox News” ta nakalto tsohon jami’in  hukumar leken asirin HKI yana cewa; Donald Trump ya janye taimakon da yake bai wa Tel Aviv.

Har ila yau, jami’in na HKi ya ce; Tel Aviv tana cikin kidima saboda dalilai da dama da su ka hada da kasa sanin yadda za ta yi da Yemen.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta kulla yarjejeniyar sayen makamai ta dala biliyan 142 da Saudiyya
  • Gwamnatin Netanyahu Tana Yi Wa Gwamnatin Trump Leken Asiri
  • Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
  • China Da Amurka Sun Yarda Da Rage Harajin Kayayyakinsu Domin Sasanta Rikicin Kasuwanci
  • Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka
  • Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul
  • Yadda ɓallewar ƙasashen AES ta illata ECOWAS
  • Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta