Nukiliya : Babu Wani ‘Musayar Sako’ Tsakaninmu Da Amurka_ Araghchi
Published: 30th, January 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba.
Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi.
Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta.
“Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.”
An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran.
“A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta aiwatar da ita, amma su ne suka kawo cikas,” in ji Araghchi, yana mai nuni da ficewar Amurka daga yarjejeniyar a shekarar 2018 a wa’adin mulkin farko na Trump.
Bayan ficewarta ne kuma gwamnatin Amurka ta kakabawa Iran sabbin takunkumai a wani mataki na matsin lamba ga Iran, lamarin da ya fusata Iran ta shiga tafiye-tafiyenta tare da soke aiki da wasu bangarori na yarjejeniyar ciki har da tace urenium din dinta son rai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta
A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran ta hanyar lumana.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa ci gaba da tattaunawa da Amurka a yayin da ake ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri yana gwada tsarin tattaunawar ba shi da ma’ana. Ya yi kakkausar suka ga matakin da hukumar ta IAEA ta dauka, inda ya yi la’akari da hakan a matsayin wani dalili na halasta cin zarafi a kan cibiyoyin nukiliyar Iran.