Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano
Published: 12th, May 2025 GMT
Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta rufe wasu gidaje biyu da ke zaman ɗakunan kwanan ɗalibanta mata a Jihar Kano.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Hotoro da titin UDB a Kano saboda zargin rashin ɗa’a.
Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCLWannan jami’i da ke kula da ɗakunan kwanan, Hamza Garba, ya ce an ɗauki matakin ne a ƙoƙarin da jami’ar take yi na tabbatar da aminci da tsaro da kuma daƙile duk wata kafa ta aikata masha’a a tsakanin ɗalibai.
Jami’ar ta ce cikin dalilan da ta ɗauki wannan mataki akwai ayyuka na rashin ɗa’a, ƙarancin ruwa da wutar lantarki, tashin-tashina da kuma tsugunar da waɗanda ba su cancanta ba a gidajen.
Sanarwar ta buƙaci ɗaliban da ke zama a gidajen biyu da su tattara komatsai da zarar sun kammala jarrabawar zangon farko.
Kazalika, sanarwar ta yi kira ga iyayen ɗaliban da cewa kada su zargi jami’ar kan duk abin da ya faru da ’ya’yansu da suka bijirewa wannan umarni.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a shekarar 2022 ce jami’ar ta Maryam Abacha ta samu lasisin soma gudanar da harkokin karatu amma har kawo yanzu ba ta tanadi ɗakunan kwanan ɗalibai a cikinta ba.
Sai dai jami’ar ta ƙulla yarjejeniya a hukumance da wasu masu gidaje da ke bayar da haya domin tsungunar da ɗalibanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗakunan Kwana Ɗalibai Jihar Kano ɗakunan kwanan
এছাড়াও পড়ুন:
Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.
Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.
Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroRahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.
Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.
Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.
Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.
Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.