Hisbah ta kama masoya kan yin aure ba tare da amincewar iyayensu ba
Published: 30th, January 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba.
A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin amaryar.
Ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’idar Musulunci kuma ba za a yarda da irin wannan lamarin ya ci gaba da faruwa a Kano ba.
“Muna sanar da cewa mun kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don kama abokansu da duk wanda ya taimaka wajen wannan auren na sirri domin hana irin wannan faruwa a gaba,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu sanya ido kan irin waɗannan al’amura, tare da yaba wa waɗanda suka kai rahoton lamarin ga hukumar.
Ya ce tuni hukumar ta fara bincike kan lamarin domin sanin matakin da za ta ɗauka a kan ma’auratan.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp