Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare.

Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine.

Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa ​​a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.

 

Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran zai kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya a yankin.

 

An yi hakan ne da nufin bai wa jama’a damar samun kula da lafiya mai inganci cikin sauki, domin inganta jin dadinsu baki daya.

 

A shirye-shiryen kaddamar da shirin, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Majalisar, Honarabul Bashir Adamu Nababa, ya gana da Darakta-Janar na KADCHMA, Mallam Abubakar Hassan, inda suka tattauna kan muhimman matakai na aiwatarwa, sannan aka mika fom din rajista domin raba su ga wadanda aka zaɓa a cikin gundumar Makera.

A bayaninsu, jami’an shirin sun jaddada kudurin shugaban majalisar na ganin al’umma ta amfana, inda suka bayyana wannan tsarin kiwon lafiya a matsayin wata shaida ta jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Ana sa ran cewa shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na gundumar za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da rajistar cikin sauki da gaskiya a cikin makonni masu zuwa.

 

Shamsuddeen Munir Atiku 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 
  • China Da Amurka Sun Yarda Da Rage Harajin Kayayyakinsu Domin Sasanta Rikicin Kasuwanci
  • Nijeriya Ta Biya Dukkanin Bashin IMF Na COVID-19
  • Burtaniya Ta Gabatar Da Sabbin Tsare-Tsare Na Shige Da Fice Da Kuma Bisar Shiga Kasar
  • Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha
  • Ma’aikatar Kasuwanci: Sanarwar Da Sin Da Amurka Suka Fitar Muhimmin Mataki Ne Na Warware Sabaninsu
  • Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Saudiya A Jiya Asabar
  • Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu