A jiya ne uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matar shugaban kasar Brazil Rosângela da Silvaa wadda ta rako mai gidanta a ziyarar da yake yi a kasar Sin, suka ziyarci babban zauren nuna fasahohin nishadantarwa ta kasar Sin, inda suka kalli abubuwan dake ciki, tare da kallon wasan opera da wasu wake-waken Sin da Brazil.

Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Brazil suna mu’amala da juna a fannin al’adu, kuma jama’ar kasashen biyu suna ta kara fahimtar juna, da sada zumunta mai zurfi. A nata bangare kuwa, Madam Rosângela ta jinjinawa nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu da kuma yadda ake raya al’adun kasar. Tana fatan kara sa kaimi ga yin mu’amala a tsakanin kasashen biyu a fannin al’adu, da kuma ci gaba da bayar da gudummawarta ga zurfafa zumunta a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

 

Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba. (Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi
  • Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin
  • Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Batun Rashin Lafiyar Tinubu
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu
  • ‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno
  • An Maka Gwamnatin Neja Da NBC A Kotu Kan Barazanar Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM