HausaTv:
2025-07-06@13:26:13 GMT

Ambaliyar Ruwan Sama Ya Ci Mutane Fiye Da 48,0000 A Somaliya

Published: 14th, May 2025 GMT

Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu.

Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da cewa da akwai yiyuwar a kara samun saukar mamakon ruwa sama a tsakiyar kasar, nan da wasu kwanaki masu zuwa.

Wannan ambaliyar dai wacce ta shammaci mutanen kasar, a lokacin da kungiyar agajin kasar ta sanar da cewa, tana da karancin kayan da ake da bukatuwa da su domin kai daukin gaggawa idan hakan ta faru.

Kasar Somaliya ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a 2023 wanda ya yi sanadiyyar  mutuwar mutane fiye da 100, da kuma tilastawa mutane fiye da miliyan 1 yin hijira.

Sauyin yanayi yana daga cikin muhimman dalilan faruwar ambaliyar ruwa irin wannan.

Yankin zirin Afirka da gabashinta, suna cikin wuraren da sauyin yanayi yake haddasa kamfar ruwa a baya da kuma fari,da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dabbobi masu yawa. Hakan nan kuma ya tilastawa mutanen yankin barin matsugunansu zuwa sansanonin ‘yan hijira domin samun abinda za su ci.

 

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ambaliyar ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliya da iska sun lalata gidaje 171 a Gombe — SEMA

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), ta ce ambaliya da iska mai ƙarfi sun lalata gidaje 171 a wasu yankunan jihar cikin watanni biyu da suka wuce.

Wannan iftila’in ya jawo asara da kuma rasuwar yara huɗu.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa

Sakataren hukumar, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne, ya bayyana wa manema labarai a Gombe cewa ambaliya da iska sun shafi ƙananan hukumomin Dukku, Kwami, Gombe da Akko.

Ya ce: “An samu rushewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe, da kuma 27 a Akko.

“Haka kuma wata coci ta lalace. Mafi yawan mutanen da suka mutu yara ne guda huɗu.”

Ya ce rashin tsaftar muhalli da sare bishiyoyi na taimakawa wajen haifar da irin wannan iftila’i.

Ya roƙi mutane da su guji zubar da shara a cikin magudanan ruwa, su kuma yi amfani da wuraren da gwamnati ta tanada domin zubar da shara.

“Dole ne kowa ya taimaka wajen kare muhalli, musamman a lokacin damina. Iyaye su kula da yara domin guje wa hatsari,” in ji shi.

Abdullahi ya kuma nuna damuwarsa kan yadda mutane ke sare bishiyoyi don yin gawayi da girki, inda ya bayyana cewa hakan yana kawo fari da lalacewar muhalli.

Ya shawarci mutane da su yi amfani da damina wajen dasa bishiyoyi a gidaje da unguwanni domin rage hatsarin iska da kuma hana ƙara yaɗuwar hamada.

Hakazalika, ya ce SEMA na shirin kai kayan agaji ga mutanen da ambaliya da iska suka shafa a sassan jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
  • Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka
  • Akalla Mutane 52 Suka Rasa Rayukansu Saboda Ambaliyan Ruwan Sama A Jihar Texas Na Kasar Amurka
  • Kungiyar Hamas Ta Sanar Da Matsayinta Kan Shirin Dakatar Da Bude Tsakaninta Da Gwamnatin Mamayar Isra’ila
  • Ambaliya da iska sun lalata gidaje 171 a Gombe — SEMA
  • Janar Ali Fadli: IRGC Suna Da Damar Kera Makamin Nukiliya Da Kuma Rufe Mashigar Ruwan Hurmuz
  • Jalali: Mun  Hana Fitowar Sanadarorin Nukiliya Ta Hanyar Aiki Da Ka’idojin Tsaro
  • NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku
  • Lakurawa sun kashe mutane 15 a Sakkwato
  • Lukurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato