A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa.

Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa.

Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1.

Kafar watsa labaru ta Axios ta ce; Babu wata ajanda a ziyarar ta Donald Trump zuwa kasashen larabawan da ta wuce ta kudi.”

Bugu da kari wani jami’in a yankin kasashen larabawan tekun pasha ya fada wa wannan kafar watsa labarun cewa; Kasuwanci shi ne babbar ajandar ziyarar Donald Trump.”

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya yi alkawalin zuba hannun jari na dalar Amruka biliyan 600 a cikin shekaru 4 masu zuwa. Haka nan kuma Saudiyyar za ta sayi makamai na dala biliyan 100 daga Amurkan.

Ita ma kasar Qatar za ta zuba jarin dala biliyan 200 zuwa 300 a Amurka, kamar kuma yadda za ta sayi jiragen saman a kasuwanci da kudinsu zai kai dalar Amurka biliyan 2.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi alkawalin zuba hannun jari na dala tirliyan 1.4 a Amurka a cikin shekaru 10 masu zuwa.

A halin yanzu shugaban kasar ta Amurka ya cire batun kulla alaka a tsakanin Saudiyya da HKI daga cikin manufofin ziyarar tashi saboda yakin da ake ci gaba da yi a Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: shugaban kasar

এছাড়াও পড়ুন:

Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno

Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno.

Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin.

Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun suna zaune ne a gaban motar  jigilar mangoro, kirar Toyota Hiace da ta dauko su daga Damboa zuwa Maiduguri.

Sun kara da cewa tashin bom din ya haifar da sabuwar damuwa game da lafiyar matafiya a kan hanyar.

Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano

Wata majiya a karamar hukumar Damboa ta tabbatar da cewa mamatan jami’an Hukumar Ilimi na Karamar Hukumar Damboa ne.

Tuni jami’an tsaro suka killace yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya kasance.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya
  • Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno
  • Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya
  • Burtaniya Ta Gabatar Da Sabbin Tsare-Tsare Na Shige Da Fice Da Kuma Bisar Shiga Kasar
  • Yanzu-yanzu: Matatar Man Dangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur
  • Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
  • Putin  Na Rasha Ya Gana Da Shugabannin Afirka Akan Batun Tsaro
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Saudiya A Jiya Asabar
  • Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari