Gwamnatin kasar Burtaniya ta gabatarwa majalisar dokokin kasar sabbin tsare-tsare na shigar kasar ta hanyoyi daban-daban.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Firai ministan kasar ta Burtania Keir Starmer yana fadar cewa abinda yake gabatarwa Majalisar don neman amincewarta, wani tsari ne wanda zai kawo tsabta a harkokin bada Visar shiga kasar Burtaniya daga kasashen duniya daban-daban.

Starmer ya kara da cewa kafin haka tsarin shige da fice a kasar ta zama a tarwatse yake. A halin yanzu bayan samar da wadannan tsare-tsare masu zuwa kasar Burtania ko wadanda suke son zama a kasar dole ne su zama masu amfanar kasar,. Da farko dole su iya turancin ingishi da wasu abubuwan da zasu taimawa ci gaban kasar.

Kafin haka dai kididdiga ta nuna cewa zuwa cikin watan Yunin shekarar da ta gabata kadai mutane kimani 906, 000 suka kaura zuwa kasar. Wanda ya ninka na shekara ta 2019 har sau 4.

Yan Najeriya dai na daga cikin wadanda suke kaura zuwa kasar Burtaniya, ko don karatu ko aiki.

 Mai yuwa wannan sabon tsarin yana iya shafar kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar.

An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙara tsaurara tsaro a makarantu a faɗin ƙasar nan.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan duba tsarin tsaro na yanzu a makarantu, musamman waɗanda ke yankunan da ke da ƙalubale, tare da gano wuraren da ake buƙatar gaggawar gyara.

CP Bello Yahaya ya tabbatar da kudirin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya na ci gaba da kare cibiyoyin ilimi, yana mai cewa makarantu dole ne su kasance wurare masu aminci domin koyo da koyarwa.

Ya jaddada muhimmancin yin nazarin tsaro a kai a kai, tsara matakan rigakafi, da kuma tabbatar da ci-gaba da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin makarantu, Ma’aikatar Ilimi da hukumomin tsaro.

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta ƙara karfafa sintiri, sa ido, da kuma gaggawar amsa kira a yankunan makarantu da aka fi ganin haɗarin tsaro.

Ya kuma bukaci shugabannin makarantu su riƙa kasancewa a shirin tuntuɓar ofisoshin ’yan sanda mafi kusa, tare da hanzarta ba da rahoton duk wani abin da ya haifar da zargi.

Ya yaba wa shugabannin ANCOPSS bisa jajircewarsu wajen aiki tare da hukumar ’yan sanda domin ƙarfafa tsaro a makarantu.

A nasu ɓangaren, shugabannin ANCOPSS sun gode wa rundunar ’yan sanda bisa ƙoƙarin da take yi na tabbatar da lafiyar dalibai da malamai, tare da alƙawarin yin aiki kafada da kafaɗa da rundunar da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa duk tsare-tsaren tsaro a makarantun sakandare.

Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma, da mazauna unguwanni da su kasance masu lura da faɗakarwa, tare da tallafa wa duk wani yunƙurin inganta tsaro a makarantu, domin kiyaye rayuwar ɗalibai nauyi ne da ya rataya a kan kowa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa
  • Mali: An Dakatar Da  Aikin Kafafen Watsa Labarun Faransa Biyu A Cikin Kasar Mali
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
  • Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe