A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi.

 

“Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri.

 

“Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.

00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141.

 

“Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala, In Sha Allahu.

“Ga waɗanda suka ci gajiyar wannan shirin, ina tunatar da kuma gargaɗar ku da kada ku yi amfani da wannan kuɗi wajen biyan buƙatun cikin gida da aka saba yi, wannan ƙarfafawa ce da nufin ba ku damar saka hannun jari a nan gaba don tallafa wa kanku da iyalanku da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikinmu na gida da ma ƙasa baki ɗaya.

 

“Ina kira gare ku da ku yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace, ku saka hannun jari a harkokin kasuwanci, kuma ku zama masu dogaro da kai.”

 

Gwamnan ya gode wa Gwamnatin Tarayya, da abokan hulɗa, da masu ruwa da tsaki, musamman ma ofishin bayar da tallafin kuɗi na ƙasa, bisa jajircewa da bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin.

 

“Bari na yi amfani da wannan dama domin tabbatar muku da cewa gwamnatinmu za ta ci gaba da haɗa kai da kowane mutum ko ƙungiya domin ci gaban jiharmu.

 

“Da wannan nake farin cikin ƙaddamar da raba katunan cirar kuɗi don sauƙaƙe biyan kuɗin Cash Transfer ga waɗanda suka cancanta.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.

Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.
Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu?

NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace

Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Faduwar Darajar Kuɗi Na Kara Tsananta Kalubale Ga Kotunan Shari’a — CJN
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi