Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya Rasu
Published: 13th, May 2025 GMT
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero.
Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya.
NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APCTuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna.
Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Masarauta Ramalan Yero Rasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba.
Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan.
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiYa ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa iyayen yara da al’ummar Kebbi cewa ’ya’yansu sun dawo lafiya.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro, musamman sojoji, ’yan sanda, da Civil Defence da suka yi aiki tukuru har aka kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamnan.
Idris ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi ba ta biya kuɗin fansa ba, “Mu, a matsayin gwamnati, ba mu ba da ko sisi ba. A binciken da muka yi, babu wanda ya biya kuɗin fansar yaran.”
A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yqn bindiga suka sace ɗaliban su 25 daga makarantar bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar.
Sai dai daga bisani ɗaya daga cikin ɗaliban ta gudo ’yan kwanaki bayan sace su.