Iran: Babban Kwamandan Sojojin Ruwa Na JMI Yace Sojojinsa A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Makiya
Published: 13th, May 2025 GMT
Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda shi da wasu manya manayan jami’an sojojin kasar suka kai ziyarar ganewa kansu irin shirin da sojojin kasar suke ciki a tashoshin jiragen ruwa da suke gabar tekun Farisa da kuma arewacin mashigar ruwa ta Hurmus
Tare da manjo janar Bakiri dai akwai kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, sai kuma Manjo Janar Hossein Salami shugaban Lundunonin IRGC da kuma wasu manya-manyan jami’an sojojin kasar.
A wani labarin kuma Janar Salami babban kwamandan sojojin IRGC gaba daya ya bayyana cewa Iran zata kai hari a kan duk wani wurin da makami ya rashi zuwa kasar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, an gano wani dutsen da aka yi sassaka kan sa a kan tsaunin Qinghai-Tibet, wanda ya kasance irinsa daya tilo na daular Qin da har yanzu ke mazauninsa na asalin, kuma a wuri mafi tsawo.
Dutsen wanda ke arewacin bakin tabkin Gyaring na gundumar Maduo, dake arewa maso yammacin lardin Qinghai, na wuri mai tsawon mita 4,300.
Gano dutsen na tattare da wata muhimmiyar daraja ga tarihi da fasaha da kimiyya. Sarki Qinshihuang na daular Qin ne ya fara hada kan kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp