Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A Kano
Published: 13th, May 2025 GMT
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki.
Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa.
Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba.
Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Aikata Rashin Ɗa a Ɗalibai Jami ar Maryam Abacha Rahotanni
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta ce tattaunawa ta hudu da Amurka tana da wahala amma tana da amfani
Iran ta bayyana cewa tattauanwa ta hudu data wakana tsakaninta da Amurka tana da wahala amma kuma tana da amfani.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce zagaye na hudu na tattaunawar da Amurka abu ne mai wahala amma mai amfani ce.
M. Baghaei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a karshen zagaye na hudu na shawarwarin Tehran da Washington a babban birnin Muscat na kasar Omani yau Lahadi.
Ya kara da cewa Oman ne za ta sanar da lokaci da wurin da za a gudanar da shawarwarin na gaba.
A nata bangare Amurka ta bakin wani babban jami’inta da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, sakamakon zagaye na hudu da aka yi da Iran kan shirin nukiliyar kasar ya karfafa gwiwar Amurka.
Tattaunawar da aka yi a birnin Muscat karkashin jagorancin wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ta dauki fiye da sa’o’i uku,” in ji jami’in.
“Sakamakon tattaunawar da muka yi a yau ya ba mu kwarin guiwa, muna kuma fatan haduwarmu ta gaba nan gaba kadan,” in ji shi.