Leadership News Hausa:
2025-05-17@04:33:52 GMT

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

Published: 1st, February 2025 GMT

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

 

Ga Yadda Za Ku Yi.

Da farko dai za ki tanadi AloeBeranki wanda ya rika, sai ki wanke shi, ki dare shi don cire wannan yaukin da ke cikinsa ki saka shi a roba Mai tsafta. Bayan kin saka a roba ko kwano,sai ki samo blender, ki markada shi, idan ya markadu ya na dawowa fari, sai ki zuba a kwano.

Sannan ki samu Sabulun base din ki ana sayar da shi a shagon sayar da chemicals, da kin ce kina son Sabulun base za su ba ki.

Ki yayyanka Sabulun base din cikin kwanon silber.

Ki kunna gas din ki ko gawayi sai ki dora ruwa a tukunya ki sa ruwan daidai yadda idan kika saka kwanon silber din da kika sawa Sabulun base zai shiga.

Idan ruwan ya yi zafi sai ki saka kwanon silber din cikin tukunyan kamar turarawa kenan, sai ki yi ta juya Sabulun zai narke, idan ya narke, sai ki sauke ki saka markadadden Aloe Beran ki ciki.

Idan kin saka ki juya ki dauko bitamin E Capsule din ki, za ki iya samun shi a chemist idan kika ce kina son bitamin E Capsule za a baki sai ki yanka shi sai ki saka ruwan cikin hadin ki, ki kawo Kala ko food colour ki saka a ciki don ya ba da kalar Aloe Bera, ki jujjuya hadin har sai sun hadu

Sai kuma ki samo roba wacce za ta ba ki shape din da kike so, ki goge da mai don Sabulun ya fita da sauki.

Ki shafa Mai a robar, ko ta Ice cream ce sai ki zuba hadinki cikin robar, amma kar ki zuba ta a lokacin da take da zafi sosai saboda kar ta kone miki roba, sai ki bar ta ta sha iska za ki iya barin ta ta kwana daya ko ta wuni.

Daga nan sai ki cire ki mata packaging Mai kyau. Shi Kenan Sabulun ki ta yi hadu sai sayarwa.

Za ki iya tallata abinki a kafofin sada zumuntar zamani (Social media)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • GORON JUMA’A 16/05/2025
  • Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar
  • Saudiya Ta Samar Da Wata Manhaja Ta Kiwon Lafiyar Mahajjata A Cikin Harsun 8 A Duniya
  • Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
  • Qalibaf : Dole ne Iran da Aljeriya su hada kai don saukaka kai kayan agaji zuwa Gaza
  • Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS
  • An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda
  • Rasha Ta Ce Putin Ba Zai Halarci Tattaunawar Zaman Lafiya A Istanbul Ba
  • JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025