Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232
Published: 16th, May 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, He Yongqian, ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da matakan kakaba harajin da ta dauka bisa binciken sashe na 232 ba tare da wani bata lokaci ba.
A yayin taron manema labaru na yau da kullum, jami’ar ta ce, harajin kwastam na sashe na 232 da aka kakaba wa motocin da ake shigar da su daga waje, da karafa, da holoko, da kuma binciken sashe na 232 kan magunguna, “zallar aiki ne na mamayar bangare daya da kuma kariyar cinikayya.
Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta gaggauta kawo karshen matakan harajin na sashe na 232, tare da magance korafe-korafen dukkan bangarori yadda ya kamata, ta hanyar tattaunawa bisa daidaito. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shuagabn Kasar Amurka Ya Sanar Da Kusancin Kulla Yarjejeniya Da Iran
Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita.
Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da ake yi a tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na makamashin Nukiliya.
Shugaban kasar ta Amurka dai ya bayyana hakan ne dai a lokacin da yake Magana da manema labaru a birnin Doha na kasar Katar.
Da yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya da Rasha, shugaban kasar ta Amurka ya kuma bayyana imaninsa da kusancin kawo karshen yakin tare da cewa yana kokarin ganin an kawo karshen rikici a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana yadda jiragen sama marasa matuki suke taka rawa a fagen yakin kasar Ukiraniya da sauran yake-yake.