Aminiya:
2025-05-14@21:57:41 GMT

’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara 

Published: 14th, May 2025 GMT

Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci.

Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.

Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo

Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su.

Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan da ya faɗi a dajin.

Ya ce ’yan bindigar sun nemi mahaifin yaron da ya miƙa musu shi, gudun ka da ya rasa sauran yaransa ya umarci yaron ya je wajensu.

Yaron ya yarda ya tafi, kuma nan take suka harbe shi har lahira.

Ɗan majalisar ya ce irin waɗannan abubuwa na nuna cewa gwamnati ta kasa kare mutane a Zamfara.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa.

Ya bayyana yadda ya yi alƙawari kafin zaɓen 2023, inda ya faɗa wa jama’a cewa sabuwar gwamnati za ta bai wa tsaro muhimmanci, amma yanzu al’amura sun ƙara lalacewa.

“Mun cuci mutanenmu. Ba sa iya zuwa gonakinsu. Tattalin arziƙinsu ya rushe. Mutane da dama sun rasa matsuguninsu, kuma babu wani taimako daga gwamnati,” in ji shi.

Ya ce ya gana da wasu shugabannin tsaro har da Ministan Tsaro, amma babu wani canji da aka samu.

“Zamfara tana cikin aminci. Yanzu kuwa, tana daga cikin wuraren da rikici ya fi ƙamari. Kundin tsarin mulki ya ce gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyi, amma hakan ba ya faruwa a yanzu.”

Da aka tambaye shi game da bai wa jama’a dama su kare kansu, sai ya ce doka ta fi komai.

“Mu ’yan majalisa ne, ba ma’aikatan tsaro ba. Ba za ce mutane su ɗauki makami ba. Amma gaskiya ne, mutane suna ganin yadda aka bar su,” in ji Jaji.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗan Majalisa jarirai Karnuka Tagwaye Tsaro Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m

Kwamandan rundunar Amotekun a Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana ƙoƙarin ceto Adepoyigi.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ondo, Olushola Ayanlade, shi ma ya tabbatar da sace shugaban na APC, inda ya ce an sace shi a gonarsa da ke hanyar Ifon-Owo.

Ya ƙara da cewa DPO na Ifon tare da mafarauta, ‘yan sa-kai da sojoji sun fara bincike domin gano inda aka kai shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
  • Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe jarirai, suka bai wa karnuka namansu a Zamfara 
  • Kwamnadan Dakarun IRGC Yace Sojojinsa A Shiye Suke Su Kare Kasar Daga Makiya
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m
  • Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno
  • ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato
  • Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
  • Mahara sanye da kayan ’yan sanda sun kashe malami sun sace mata 3 a makaranta a Zamfara