A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka
Published: 14th, May 2025 GMT
Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba.
Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da ya kamata mu lura da shi, shi ne, yayin da muke fuskantar matsin lamba daga kasar Amurka, kar mu yi kasa a gwiwa, maimakon haka ya kamata mu yi kokarin hadin gwiwa da abokan hulda.
Bayan da kasar Amurka ta kaddamar da yakin haraji, kasar Japan ita ce kasa ta farko da ta tura wakili zuwa kasar Amurka, don rokon a yafe mata harajin da aka kara. Amma ba ta samu komai ba, ta tashi a fankan-fayau balle ma a batun harajin kwastam mai matukar tsanani. Ganin haka ya sa kasar Japan ita ma ta dauki “kati”, ta fara wasa da shi, inda kasar ta sanar da cewa ba za ta taba hakuri da manufar haraji ta kasar Amurka ba. Kana jaridar Labarun Tattalin Arziki Na Kasar Japan ta wallafa wani bayani mai taken “Matakan Kasar Amurka Za Su Haifar Da Tsarin Cinikin Duniya Da Bai Kunshi Kasar Amurka Ba”.
A hakika, ana kan hanyar samun wani tsarin cinikin duniya, da bai shafi kasar Amurka ba, ko kuma ba zai tasirantu da Amurka ba. Idan mun lura da ayyukan da dimbin kasashen nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Latin Amurka suke yi, da sanarwoyin kasashen BRICS, da na kungiyar kasashen Afirka ta AU, to, za mu san cewa, kasashe masu tasowa suna kokarin karfafa hadin kansu a fannin tattalin arziki da cinikayya, da daidaita tsare-tsaren samar da kayayyaki, ta yadda za su samu sabbin damammakin raya kansu, yayin da ake fuskantar daidaituwar yanayin tattalin arzikin duniya.
Haka zalika, wata shawara mafi muhimmanci ita ce, a yi watsi da burin zama abokiyar kasar Amurka.
Saboda Amurka na kallon moriyar kanta a gaba da komai. Don haka, idan wata kasa tana son zama abokiyar huldar kasar Amurka, to, wata rana za ta ga yadda kasar Amurka ta mai da ita tamkar abokiyar gaba. Wannan dabarar kasar Amurka ta sa Ukraine rasa albarkatun kasarta, kana kasar Canada ta zama “jiha ta 51 ta kasar Amurka” a idon Amurka din. Yayin da kasashen Turai, ko da yake suke son taimakon kasar Amurka wajen dakile tattalin arzikin Sin, sai dai duk da haka, kasar Amurka na son ganin yadda kasashen Turai su nuna sassauci, da zama wani bangaren da kasar Amurka za ta iya kwatar dukiyoyinsa yadda ta ga dama. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da kasar Amurka Da Kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki
A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya kusa da doron kasa a lardunan Jiangxi, Sichuan da Guangxi inda ake fuskantar dimbin kalubalen fadada hanyoyi saboda yanayin tsaunukansu.
Tabbas, duka wadannan sun zo da wani irin sabon salo a duniya da kasashe za su yi koyi da kasar Sin wajen zamanantar da sha’anin jigilarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp