Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa
Published: 14th, May 2025 GMT
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar za ta kara inganta kula da duk wani abu mai nasaba da sarrafawa ko samarwa a bangaren ma’adanan kasa masu matukar muhimmanci, don hana fitarwa ba bisa ka’ida ba, da kuma kiyaye tsaron kasa.
Mai magana da yawun ma’aikatar wanda ya bayyana haka a yau Laraba, ya ce, karfafa yadda ake kula da fitar da albarkatun ma’adanai masu muhimmanci zuwa ketare yana da muhimmanci ga tsaron kasa da muradun ci gaba.
A ranar Litinin da ta gabata ne, wani taron kasa da aka kira a Changsha, babban birnin lardin Hunan, ya jaddada bukatar karfafa “kula da cikakken tsarin fitar da manyan ma’adanai masu muhimmanci zuwa kasashen waje.” Taron ya samu halartar jami’ai daga hukumomin gwamnatin tsakiya 10 da yankuna bakwai masu arzikin muhimman ma’adanai, ciki har da jihar Mongoliya ta gida da lardin Jiangxi.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa, “Domin hana fitar da ma’adanai masu muhimmanci ba bisa ka’ida ba, dole ne a fara kula da lamarin daga tushe kuma a karfafa shi a dukkan sassan harkar ma’adanai, da suka hada da hakawa, narkawa, sarrafawa, sufuri, masana’antu, sayarwa, da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia
Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu.
Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune.
Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — FayemiKamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta yankin Arewa, wacce ta ƙaddamar da bincike kan ayyukanta a watan Yulin 2022 bayan samun bayanai daga ’yan sandan Ƙueensland.
A cewar AFP, “Wani gungun ‘yan asalin Papua New Guinea (PNG) da suka yi ƙaura zuwa Australia don yin karatu, an yi zargin cewa an tilasta musu yin aiki ba tare da son ransu ba a gonaki.”
An ba da rahoton cewa matar mai izinin zama ƙasashen biyu ta yaudari aƙalla ƴan ƙasar PNG 15, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 35, zuwa Australia tsakanin Maris 2021 da Yuli 2023 ta hanyar kamfaninta, BIN Educational Serɓices and Consulting, da kuma ta hanyar ba da guraben karatu na bogi.
Rahoton ya bayyana cewa, shafin intanet na kamfaninta ya yi iƙirarin bayar da “daidaitaccen tsarin zamani don ilimi, horarwa da kuma aikin yi.”
Sai dai ’yan sandan sun ce gaskiyar lamarin ya sha bamban sosai.
Da zarar sun isa Australia, an yi zargin cewa an tilasta wa ɗaliban su sanya hannu kan jerin takaddun doka da ke tilasta su su biya kuɗin da ke da alaƙa da karatun, kuɗin jirgi, aikace-aikacen samar da biza, inshora da kuma kuɗaɗen doka.”