Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Da Jirgin Alhazan Kano Na Farko
Published: 15th, May 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan jihar Kano da ke niyyar gudanar da aikin hajjin bana.
Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu na gari a jihar, su kuma yi addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da hadin kan jihar Kano da Nijeriya baki daya.
Ya jaddada kudirin gwamnati na tallafa wa duk maniyyata a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki.
Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ya shawarci alhazai da su kwantar da hankulansu, su kuma maida hankali wajen gudanar da ibada.
A nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa jirgin na farko ya hada da mahajjata daga kananan hukumomi goma sha daya (11):
Ajingi: Mahajjata 15 (maza 10, mata 5)
Tofa Mahajjata 17 (maza 12, mata 5)
Tudun Wada: Mahajjata 115 (maza 84, mata 31)
Karamar Hukumar Doguwa: Mahajjata 94 (maza 73, mata 21)
Karamar Hukumar Bebeji: Mahajjata 82 (maza 67, mata 15)
Garin Malam: alhazai 47 (maza 33, mata 14)
Gaya: Mahajjata 14 (maza 10, mata 4)
Karamar Hukumar Madobi: Mahajjata 36 (maza 21, mata 15)
Karamar Hukumar Kabo: Mahajjata 18 (maza 13, mata 5)
Wudil 36 Alhazai
(Maza 30, mata 6)
Rimin Gado: Mahajjata 33
Karin bayani: Jami’an gwamnati 15 da jami’an kasa 10 ne ke raka mahajattan domin kula da ayyukan alhazai.
Alhazai 560 ne ake jigilarsu a wannan jirgi na Max Air zuwa filin jirgin saman Yarima Mohammed Bin Abdulaziz dake Madina, wanda ya tashi da misalin karfe 12:11 na rana laraba.
Alh. Lamin Rabi’u Danbappa ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif ta yi duk wani shiri da ya dace domin tabbatar da walwala da jin dadin alhazai.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka hada da shugaban hukumar gudanarwar hukumar Alhaji Yusif Lawan, da ‘yan kwamitin, kwamishinoni, da masu ba da shawara na musamman.
Abdullahi jalaluddeen Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Karamar Hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin.
Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida.
’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun TuraiWani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu mata biyu daga Tsundu mai makwabtaka.
Ya ce al’ummar garin sun yi ƙoƙarin daƙile harin amma suka kasa saboda ƙarancin makamai, duk da cewa sun sanar da ’yan sanda da sojoji tun kafin faruwar harin bayan samun bayanan cewa ’yan bindigar na dosar yankin.
Ya roƙi gwamnati ta ɗauki mataki wajen ceto mutanen da aka sace da kuma kare rayukan mazauna yankin.
Aminiya ta yi ƙoƙarin ji ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, sai da har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.