NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC
Published: 15th, May 2025 GMT
Ƴan majalisar tarayya guda biyu daga jihar Kano, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun sanar da barin jam’iyyar NNPP zuwa APC a yayin zaman majalisar ranar Alhamis, suna mai nuni da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar.
Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun ficewarsu a zaman majalisar, inda ya bayyana cewa Usman na wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya, yayin da Sani na wakiltar Karaye/Rogo.
Ko da a kwanan baya ma Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da wasu sun fice daga jam’iyyar NNPP, su ma dai sun ce rikicin ne ya fitar da shi.
Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje da wasu manyan ƙososhin jam’iyyar sun halarci taron sauyin sheƙar a majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kashi Na Biyu Na Maniyyata 415 Daga Jihar Kwara Sun Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya.
Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki.
Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya.
An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin jirgin sama na Babatunde Idi-Agbon dake Ilorin.
Ya zuwa yanzu dai an jigilar alhazai 975 daga jihar Kwara zuwa kasar Saudiyya.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU