Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Gaza
Published: 14th, May 2025 GMT
A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51
Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51, ciki har da 45 a arewacin zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinawan “WAFA” ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudanci da arewacin zirin Gaza ya kai 51 tun da tsakar daren jiya, ciki har da shahidai 45 a arewacin zirin Gaza.
Wannan kisan kiyashi na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila, da kuma kasancewar shugaban Amurka Donald Trump a halin yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, inda yake cewa: Al’ummar Falasdinu a Gaza sun cancanci kyakkyawar makoma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Bukatar Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza. Ya yi kira da a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta tare da baiwa Falasdinawa ‘yan gudun hijira ‘yancin komawa kasarsu ta gado.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ratsa ta wasu kasashen musulmi, kuma lokaci ya yi da kasashen musulmi za su tilasta wa wannan gwamnatin mamaya ta hanyar yanke shawarar gama-gari don kawo karshen killace Gaza.