Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan

Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin da jirgin sama maras matuki ciki ya yi niyyar kai wa kan mafi girman sansanin sojin ruwan kasar da sanyin safiyar Laraba, in ji wata majiyar soji. Wannan dai shi ne rana ta hudu a jere da ake kai hare-hare kan birnin Port Sudan da ke karkashin ikon gwamnati.

Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta ce, jiragen saman yakin marasa matuka ciki sun kai hari kan sansanin sojin ruwa na Flamingo, kuma na’urorin kakkabo makamai masu linzami suna kakkabo makaman da aka harba. Tsawon rabin sa’a ana jin karar makaman roka masu linzami da aka yi amfani da su a kasa da kuma wasu bama-bamai da suka samo asali daga arewacin Port Sudan, inda sansanin sojin ruwa yake.

Port Sudan dai ita ce wurin zama na wucin gadi na gwamnatin kasar, lamarin da ya sanya ta zama hedkwatar rikon kwarya bayan barkewar yaki tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

Tun a watan Afrilun shekara ta 2023 ne Sudan ta fada cikin kazamin rikici tsakanin kwamandan sojojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda shi ne shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin kasar tun bayan juyin mulkin shekarar 2021, da kuma tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, kwamandan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai

Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya.

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su.

Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya

Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa.

Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka kai su tsibirin na Lampedusa, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a kasar ta Italiya ta tabbatar.

Kakakin Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), Flavio Di Giacomo, ya ce akwai mutum 95 a cikin jiragen guda biyu da suka nitse.

Ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, “kasancewar an ceto mutum 60 da rai, ana fargabar akwai mutum 35 da suka mutu ko kuma suka ɓace.“

Hatsarin wanda ya ritsa da ’yan ci-ranin da suka taso daga ƙasar Libya shi ne na baya-bayan nan ga mutanen da ke kokarin tsallaka teku domin shiga nahiyar Turai.

Alkaluma sun nuna daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, akalla mutum 675 ne suka rasa ransu ta irin wannan hanyar a kan iyakokin kasashen biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan
  • ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai
  • Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwaman Zamfara
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida 
  • Iran: Janar Hatami ya karbi bakuncin babban hafsan hafsoshin sojin Afirka ta kudu
  • An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe
  • Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fushin Sojojin Kasar
  • Jiragen saman NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 592, Sun Lalata Kayayyakin Yaki 372
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 400 a Zamfara