Aminiya:
2025-05-14@18:06:17 GMT

Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi

Published: 14th, May 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa da shi da Sule Lamido har yanzu suna kan kujerar mulki, da sun fito ƙarara sun ƙalubalanci Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Amaechi ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna ‘Being True to Myself’ da aka gudanar a Abuja.

Ko yanzu aka yi zaɓe Tinubu ne zai yi nasara — Oshiomhole DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya

“Da mun fito da ƙarfinmu, mun ƙalubalanci gwamnati, mun kalubalanci shugaban ƙasa,” in ji Amaechi.

“Haka muka saba a lokacin muna Gwamnoni. Muna da kishin ƙasa da ƙwarin gwiwar sauya al’amura.”

Ya bayyana yadda dangantakar siyasar da ke tsakaninsa da Lamido, inda ya ce duk da kasancewar suna da alaƙa a wancan lokaci, sun raba gari ne lokacin da Lamido ya ƙi komawa jam’iyyar APC domin su haɗa ƙarfi wajen kayar da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

“A lokacin, Lamido ya zaɓi kafa sabuwar jam’iyya – SDP, amma mu mun yarda cewa za mu fi samun nasara a jam’iyyar APC,” in ji Amaechi.

“Wannan ne ya sa hanyoyinmu suka rabu.”

Shugaba Tinubu, wanda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya wakilta a taron, ya ce shugaban ƙasa ya amince da mahawara mai ma’ana, amma hakan ba zai hana shi yi wa ƙasar nan abin da ya dace ba.

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ma ya yi jawabi a wajen taron, inda ya bayyana Lamido a matsayin jagoran da ke da gaskiya da tsayawa kan aƙidarsa, inda ya ce lokacin da Lamido ke Ministan Harkokin Waje, ya taimaka wajen dawo da mutuncin Najeriya a idon duniya.

Obasanjo ya ce, “Sule ya taɓa faɗa, ‘Idan ka ga ban cancanta ba, ka ba ni minti biyar kawai na yi murabus. Amma ka da ka tambaye ni takardar murabus da ba ta da kwanan wata.’ Na girmama wannan matsayi nasa.”

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya wakilci Janar Abdulsalami Abubakar, ya jinjina wa littafin Lamido da cewa ya bayyana tarihin siyasar Najeriya da darusan da matasa za su amfana da su.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Iyorchia Ayu, wanda ya yi nazari a kan littafin, ya soki gwamnatin APC da cewa ta zama annoba ga Najeriya.

Ya buƙaci Lamido da ya ci gaba da rubuta littattafai domin su zama jagora ga ’yan Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jigawa Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar  tsagaita budewa juna wuta.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce kawo karshen zubar da jinni tsakanin kasashen biyu na fiye da shekaru uku da suka gabata.

Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, haduwar shuwagabannin biyu zai fayyace matsayin yakin, da kuma yiyuwar dakatar da shi nan kusa. Banda haka haduwarsu zai bawa kasar Amurka damar gane matakin da zata dauka nan gaba, haka ma tarayyar turai.

Kafin haka dai a ranar Asabar da ta gabata ce, shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayyana cewwa, Rasha a shirye take ta bude tattaunawa gaba da gaba da kasar Ukraune a birnin Istambul na kasar Turkiyya a ranar 15 ga watan mayun da muke ciki wato ranar Alhamis mai zuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ko yanzu aka yi zaɓe Tinubu ne zai yi nasara — Oshiomhole
  • Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
  • Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil
  • Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba
  • NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Matsayin Kasarsa Na Tattaunawa Da Amurka
  • 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido 
  • Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul
  • NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO