Kashi Na Biyu Na Maniyyata 415 Daga Jihar Kwara Sun Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
Published: 15th, May 2025 GMT
Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya.
Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki.
Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya.
An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin jirgin sama na Babatunde Idi-Agbon dake Ilorin.
Ya zuwa yanzu dai an jigilar alhazai 975 daga jihar Kwara zuwa kasar Saudiyya.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara zuwa kasar Saudiyya jihar Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya Ya Jaddada Goyon Bayan Kasarsa Ga Iran
Yarima mai jiran gadon Saudiyya ya tabbatarwa shugaban kasar Iran cewa: Saudiyya tana goyon bayan Iran
Yariman mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya tabbatar da hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Asabar, yana mai jaddada cewa: Masarautar Saudiyya da daukacin al’ummar musulmin duniya sun hadu a kan goyon bayan Iran.
Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya ya ce: Dukkanin al’ummomin kasashen musulmi a yau suna da hadin kai da jaddada goyon bayansu ga Iran, kuma yana iyaka kokarinsa a fagen diflomasiyya da matsin lamba na kasa da kasa don dakatar da wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan Iran.
Bin Salman ya yi Allah wadai da hare-haren rashin adalci da ‘yan sahayoniyya suke kaiwa Iran.
Ya kuma bayyana jimaminsa tare da jajantawa al’ummar kasar Iran dangane da wadannan hare-hare da suka rutsa da su, yana mai jaddada cewa: Saudiyya tana da tabbataccen matsayi kan tsayawa tare da ‘yar uwarta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma duniyar musulmi a yau ta hade kan muryar daya wajen goyon bayan Iran.
Ya ci gaba da cewa: “Mun yi imanin cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman ta hanyar kara kunna wutar rikici ta janyo Amurka a cikin tsakiyar rikici, amma suna da yakinin cewa martanin Iran a kan ma’aunin daidaito da matakan hankali zai dakile wannan yunƙurin makirci.”
Bin Salman ya kuma jaddada cewa: Kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da duk wani tallafi da ya dace ga ‘yan uwanta Iran.