Masu garkuwa da Shugaban APC a Ondo sun riƙe masu kai kuɗin fansa
Published: 15th, May 2025 GMT
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga.
A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi a ƙofar gidansa inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 100 kafin daga bisani a daidaita a kan miliyan biyar.
Majiyoyin sun a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gida ne maharan suka far masa suka fito da shi daga cikin motarsu, sa’annan suka make shi da gungumen ice sa’annan suka tafi da shi.
Wani makusanci ga waɗanda suka kai kuɗin ya bayyana cewa, “Bayan daidaitawa da ’yan bindigar a kan kuɗin fansa, da masu biyan kuɗin suka kai sai ’yan bindigar suka kama su suka ɗaure a cikin dajin.”
A soke sakamakon jarabawar JAMB na 2025 gaba ɗaya —Ɗalibai ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a ZamfaraDa yake tabbatar da faruwar abin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ose, Kolapo Ojo, ya ce yanzu ’yan bindigar sun ƙara yawan kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 30 kafin sakin ɗan siyasan da sauran mutanen biyu.
Sai dai ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, jami’an tsaro na yin duk mai yiwuwa domin kuɓutar da duk mutanen.
Kakakin ’yan sanda a jihar, Olusola Olayinka, ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta haɗa guiwa da jami’an tsaron sa kai da maharba domin zaƙulo ’yan bindigar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa yan bindigar
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu
Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009.
An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a MaiduguriA cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini.
Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin Iraki, tare da goyon bayan amfani da na’urorin leƙen asiri da bincike mai tsanani a matsayin martani ga harin ta’addanci na ranar 11 ga Satumba, 2001.
Bayan ya bar ofis, Cheney ya zama ɗaya daga cikin masu sukar salon jagorancin shugaban ƙasa Donald Trump a wa’adin mulkinsa na farko, musamman bayan ’yarsa, Liz Cheney, ta zama jigo cikin ’yan jam’iyyar Republican da suka fito fili suna sukar Trump, lamarin da ya zamo sila dakatar da shi daga jam’iyyar.
Liz Cheney ta kasance ɗaya daga cikin ’yan jam’iyyar da suka soki matakin magoya bayan Trump na tayar da tarzoma a ginin Majalisar Dokoki ta ƙasar (Capitol) bayan shan kaye a zaɓen ranar 6 ga Janairu, 2021.